fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Mayakan ISWAP sun kai hari a shingen bincike, sun kashe mutum 2 a Maiduguri

Akalla jami’an tsaro biyu ne suka mutu sannan wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka a lokacin da mayakan kungiyar ta’addanci ta Da’ish suka kai hari a wani sansanin soji da ke kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kamar yadda majiyar tsaro ta bayyana.

Hakan ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan da rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa ta kashe mayakan sama da 100 da suka hada da manyan kwamandojin iswap 10 a yankin tafkin Chadi.

An tattaro cewa an fara gumurzun ne da misalin karfe 6 na yamma wanda ya sa daruruwan fararen hula suka tsere daga gidajensu a unguwar Molai General a Maiduguri.

An tattaro cewa da yawa daga cikin ‘yan ta’addan a cikin motoci iri-iri da babura dauke da manyan makamai ne suka mamaye shingayen binciken jami’an tsaro na rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai da suka hada da sojoji da ‘yan sandan tafi da gidanka.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party

Manyan jami’an tsaro sun ce an kashe jami’an tsaro akalla biyu tare da jikkata wasu da dama yayin da rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai ta taimaka wa kasa wajen dakile hare-haren.

Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun yi awon gaba da wasu kayan aikin soji da suka hada da wata motar daukar bindiga da motar daukar marasa lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.