Saturday, July 13
Shadow

Mayakan Kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno.

Sun kashe masuntanne a karamar hukumar Kukawa i da kuma da yawa suka jikkata.

Lamarin ya farune da misalin karfe 10:40 na dare yayin da masuntan ke shirin fara kamun kifi na dare.

Mayakan na ISWAP sun isa wajan da masuntan suke suka zagayesu suka kuma bude musu wuta.

Wata majiya ta bayyanawa Daily Trust cewa mayakan sun sacewa masuntan kifi da yawa.

Wanda suka rasu kuma an binnesu kamar yanda addinin musulunci ya tanada.

Saidai har yanzu akwai wanda suka bace ba’a san inda suke ba.

Karanta Wannan  Yawan wanda suka mutu bayan harin kunar bakin wake sun kai 30, guda 100 sun jikkata a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *