Friday, May 29
Shadow

Mayar da Almajirai jihohinsu na Asali shine abu mafi dacewa dan kowane Yaro ya kamata ace yana gaban iyayensa>>Gwamna El-Rufai

Duk da damuwar da wasu ‘yan kasa ke nunawa game da mayar da Almajirai jihohin su na asali a wannan lokaci da ake yaki da cutar coronavirus, gwamnatin jihar Kaduna ta ce, hakan shine mafi dacewa.

 

 

Gwamnan jihar Nasiru Ahmed El-rufai wanda ya fara mayar da Almajiran dake jihar Kaduna zuwa garuruwansu ya ce, kungiyar gwamnonin Arewaci ta amince da wannan mataki. “Ya kamata ko wanne yaro ya zauna a gaban iyayensa. Kuma wannan lokacin shine daidai” in ji shi.

 

Wani abu dake ci gaba da jan hankalin al’umma game da mayar da Almajirai gida shine wasu daga cikin su sun kamu da cutar coronavirus, to amma El-rufai ya ce, mayar da Almajiran garuruwansu ya na da ma’ana a yanzu, saboda ta haka ne za su fi samun taimakon da ya dace.

 

 

Kwamishiniyar ma’aikatar mata da walwalar al’umma ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Mohd Baba ta ce, duk an kulle makarantu, kuma yaran yayon yawon su suke a gari, saboda haka ya kamata a dauki matakin da ya zama wajibi don ceto rayuwarsu.

 

 

Daya daga cikin manyan malamai masu wa’azi a jihar Kaduna Sheik Halliru Maraya ya ce, matakin mayar da Almajirai da gwamnatocin arewacin Najeriya suka dauka ya sabawa doka. Domin sashi na 41 karamin sashi na daya dokar tsarin mulkin Najeriya ya baiwa duk dan kasa damar zama ko ina a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *