fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Mazakutar mijina ta daina aiki kuma ba zan iya hakura ba>>Wata mata ta kai mijinta kotu

Wata mata me kimanin shekaru 54 me suna Blessing Mormah ta kai mijinta kotu inda tace yanzu baya iya gamsar da ita a gado.

 

Matar tace tana son a raba aurensu na shekaru 25 inda tace dama can takura mata aka yi ta auri mijin nata.

 

Matar tace ‘ya’yansu 5, amma koda yaushe suna fada, kuma duk sanda suka yi fada sai yace mata ta fita ta bar mushi gida.

 

Tace kuma maganar mazakutarsa ta kaishi asibiti an bashi magani amma yaki sha sai yace mata lafiyarsa kalau, amma idan tace ya gamsar da ita sai ya kasa.

 

Alkalin kotun ya daga shari’ar zuwa 12 ga watan Mayu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.