fbpx
Monday, March 1
Shadow

Mazauna Gari Sun Gudu Yayin Da ‘Yan Ta’addan Boko Haram suka Kai hari Askira a Borno

Dubun dubatan mazauna garin suka gudu daga gidajensu a jiya yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari garin Askira da ke karamar hukumar Askira / Uba a jihar Borno.
Bayanai sun ce maharan sun afka wa garin ne bayan Sallar Maghib inda suka yi ta harbi ba kakkautawa.
Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da harin.
Sai dai ya ce sojojin sun fafata da maharan. “Ba wanda zai iya sanin halin da ake ciki a yanzu, zan iya tabbatar da cewa da yawa daga cikin mutanenmu sun gudu daga gidajensu.
“An sanar da ni cewa sojojin suna nan suna fafatawa da su”.
Wani memba na Rundunar Hadin Gwiwar Farar Hula, Yakubu Saidu, ya ce yana jin tsoron harin bazata da maharan suka kaiwa garinsu.
“Sun zo daidai karfe 6:30 na yamma, suna ta harbi daga kowane bangare, sai muka ruga cikin daji wasu kuma suka shiga cikin gida, sun zo ne da motocin daukar bindiga kusan tara dauke da bindigar kakkabo jiragen sama.
“Tsarin tsaron mu yana yin bakin kokarin sa saboda mu ma muna jin karar harbe-harbe daga bangaren su, amma hakan bai isa ba, ya kamata gwamnati tayi wani abu game da garin mu kafin su fatattake mu baki daya,” Saidu ya yi kira.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *