Real Madrid tayi nasarar sayen daya daga cikin zakarun ‘yan wasan tsakiya na duniyar tamola watau Aurelien Tchouameni.
Madrid tayiwa dan wasan kwantirakin shekaru shida ne bayan ta sayo shi daga Monaco kuma Liverpool da Chelsea duk sun nemi dan wasan amma ya zabi Madrid.
Kuma yace nasarar da Madrid tayi na doke PSG, Chelsea da Manchester City ne tasa shi ya zabeta akan sauran kungiyoyin dake nemansa.
Sannan kuma dan wasan yace Mbappe yaso ya hana shi komawa Real Madrid domin yayi mai tayin zuwa PSG, amma sai yace masa shi Madrid yake so.