fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

Wani manomi dan shekaru 35 da haihuwa kuma mai wakiltar mazabar Iwogu a karamar hukumar Keana ta jihar Nasarawa, Ibrahim Kasimu Oboshi, wanda aka fi sani da Ogah, ya auri wasu mata biyu a rana daya. Ya auri Nazira Dahiru Ozegya da Rabi Isyaku Akose a ranar 28 ga Maris, 2020.

A lokacin da yake Magana da jaridar Daily Trust a ranar Asabar, ya ce, “Ni maraya ne, mai yin noma kuma a yanzu ni kansila ne. A matsayina na maraya, na ɗauki noma da makaranta da muhimmanci, da harkar noma ne, na sami damar kula da mahaifiyata da kaina. Daga baya ne, na ci zabe don wakiltar garina. ”

 

Ya ce lokacin da mutane da yawa suka ji yana shirin auran mata biyu, sai suka yi mamaki ko shi ɗan sarki ne ko ɗan wani attajiri ne, amma an gaya musu cewa ni manomi ne. “A gaskiya na rike noma da matukar muhimmanci fiye da wani abu wanda dashine na samu duk wani abun rayuwa. Inji shi.

 

A cewar sa kalubalan da ya fuskanta shine na yadda zai sanar da mahaifiyar sa akan shirin sa na auran mata biyu, a lokacin da ya sanar da ita, sai tace idan babu laifi a addinin musulunci babu komai, daga bisa nine wani malami ya tabbatar da cewa hakan bai sabawa Shari’a ba.

A lokacin da aka tambaye shi yadda ya hadu da duka matan ya bayyana cewa ya fara haduwa ne da Nazira a garinsu keana, daga bisani ya hadu da Rabi a Obi. Haka kuma bayan ya sanar dasu batunsa na auran su su biyu ko wacce ta amince tare da yin fata nagari.

 

Daurin aure na farko da Nazira an dau ra shine a farfajiyar Abawa da ke cikin yankin Amiri na Keana da karfe 10 na safe yayin da na biyun ya gudana ne a gidan Alhaji Ishaku Akose a yankin Odobu na karamar Hukumar Obi da tsakar rana.

 

Bayan haka, bikin liyafar ya gudana a gaban fadar masarautar gargajiya ta garin, Osana na Keana, tare da ango zaune tsakanin amaransa.

A cewar angon duk da cewa an kai matan nasa gidan sa a rana guda ya bayyana cewa Nazira ce Uwar gida.

 

A karshe Matan biyu sun ce suna farin ciki da auran su tare da mutumin da suke ƙauna kuma za su yi duk mai yiwuwa don ganin sun faranta masa rai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.