A yaune aka ga shugaban ma’aikata Abba Kyari da shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya Winnifred Oyo-Ita a gurin zaman majalisar zartarwa da akeyi duk ranar Laraba, cikin farin ciki da annashuwa, wannan labari ya dauki hankulan mutane sosai ganin cewa ana tsammanin sunyi fada.
To saidai wani abu kuma daya kara daukar hankulan mutane a daya daga cikin hotunan da aka gansu shine yanda suke matse kusa da juna, har Abba Kyarin ya kai hannu ya rungumota.
Yin hakan dai ga Abba kyarin a matsayinshi na musulmi ba daidai bane. Hakan yasa mutane da yawa dora alamar tambaya akan wannan hoto.