Wata kungiyar Inyamurai ta nemi a taimaka a musu maganin wata kungiyar IPOB data balle daga cikin uwar kungiyar.
Kungiyar inyamuran dake zaune a kasar Finland ta nemi a kama da kuma hukunta Simon Ekpa Wanda shine shugaban kungiyar ta IPOB data balle.
Ekpa ya nemi a yi zaman gida dole sannan kuma kada wanda ya fita zaben shekarar 2023.
Kungiyar tace ta dauki wannan mataki ne bayan zama da Ekpa kuma tana son a hukuntashi a kasar ta Finland da kuma gida Najariya kamar yanda shugaban kungiyar, Kingsley Orji ya bayyana a rahoton Premium times.