Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya bayyana cewa membobin jam’iyyarsa ta APC kadai zai marawa baya a zaben shekarar 2023.
Hadimin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana hakan a ranar laraba, inda yace har yanzu Buhari jigon jam’iyyar APC ne kuma zai tsayawa ‘yan takarar dake jam’iyyar suyi nasara.
Sai dai fa ba zai taba tsayawa wa’yanda basa jam’iyyar ba da kuma wa’yanda suka sauya sheka dama masu maka su a kotu bakidaya.
Amma yace yana maraba da duk wata jam’iyyar dake shirin mara masu baya sai dai su kam babu wanda zasu marawa baya face dan jam’iyyarsu.
A karshe shugaban kasar ya kara da cewa bada wata jam’iyyar adawa yake wannan maganar ba ra’ayinsa ne kawai ya fadi.