Dan wasan tsakiya na kungiyar Paris Sainy Germain, Ander Herrera ya danganta zakarun tamola watau Ronaldo da Messi.
Herrera ya buga wasa da gabadaya zakarun wasan tamolar guda biyu na duniya, saboda haka ya son su sosai.
Inda yace shima Lionel Messi kamar Ronaldo yake kuma zai iya zira kwallaye 50 a kaka mai zuwa duk da cewa baiyi kokari sosai a wannan kakar ba,
Domin har yanzu shima tauraron shi yana haskawa a gasar ta Lig one.