Kocin kungiyar Alnasr ta kasar Saudiyya, Rudi Garcia ya bayyana cewa, Lionel Messi suka so siyowa amma suka kare da sayen Cristiano Ronaldo.
Ana ganin wannan magana da yayi ka iya sawa su fara samun matsala da Ronaldo a kungiyar.
Saidai rahotanni sun bayyana cewa, barkwanci ne yake.
Ronaldo dai ya kammala komawa kungiyar ta Alnasr akan Miliyan £175.
Masoya Ronaldon sun rika kiran sunansa suna rera waka inda kuma da yawa suka taru dan sayen rikarsa me lamba 7