fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Messi ne yazo na farko yayin daya kerewa Ronaldo da Lewandowski idan da za’a bayar da kyautar Ballon d’Or

Ba za’a bayar da kyautar Ballon D’or ba a wannan shekarar. Kuma hakan na nufin cewa Messi ba zai iya kara kerewa babban abokin hamayyar shi ba wato Cristiano Ronaldo da kyautar har guda biyu bayan dama ya wuce shi da guda.

Lewandowski shima zai iya lashe kyautar saboda kokarin da yayi na cin kwallaye a wannan kakar wanda yanzu haka shine dan wasan da yafi gabadaya yan wasan kwallon kafa zira kwallaye masu yawa, yayin da kwallayen nashi suka kai 34.

Da ace za’a bayar da kyautar to hasashen da WhoScore.com suka yi ya nuna cewa Messi ne yazo na daya saboda dan wasan shine yaci kyautar Golden Boot na gasar La Liga kuma ya karya tarihin taimakawa wurin cin kwallaye a gasar, yayin da yafi gabadaya yan wasa taba kwallo a wannan kakar.

Karanta wannan  Kungiyar PSG ta kori kocinta Maurizio Pochettino

Kylian Mbappe ne yazo na biyu bayan Messi yayin da dan wasan yayi nasarar cin kwallaye 12 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye tara a wannan kakar kafin a dakatar da gasar lig 1, kuma kungiyar su aka baiwa kofin gasar.

Lewandowski shine yazo na uku a lissafin saboda kokarin da yayi na cin kwallaye a wannan kakar kuma kungiyar shi ta Munich ta lashe kofin guda biyu. Cristiano Ronaldo shine yazo na hudu a cikin jerin sunayen. Duk da cewa dan wasan yaci kwallaye 30 a wannan kakar, mutane da yawa basa tunanin cewa dan wasan zai lashe kyautar Balloon D’Or din.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.