Sunday, June 7
Shadow

Messi, Ronaldo, Neymar sune suka fi sauran yan wasan kwallon kafa daukar albashi mai tsoka

An samu labari daga wata mujallar yan wasan kwallon kafa ta faransa cewa har yanzu Ronaldo, Messi da Neymar sune yan wasa guda uku da suka fi daukar Albashi mai tsoka a duniyar wasan kwallon kafa.

 

Sun kimanta yadda suke samun kudade kamar ta wurin masu daukar hoto, da albashin su da kuma abin da suke samu a duk karshen kakar wasa da dai sauran su.
A karshe sun ce tauraron barcelona Messi shi ne yazo na daya wanda a duk shekara yana samun euros miliyan 131. Sai dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo wadda a duk shekara yana samun euros miliyan 118.
Sai tauraron PSG Neymar wanda ya bar Barcelona ya koma faransa a farashin da ba’a taba siyan wani dan wasa ba. Shine yazo a na uku wanda a duk shekara yana samun euros miliyan 95 kuma yana yana gaban dan wasan gaba na Madrid Gareth bale wanda a duk shekara yana samun euros miliyan 38.7.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *