A ranar Lahadi ne Mesut Ozil ya tabbatar da cewa zai bar Arsenal zuwa kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya bayan da ya shafe watanni yana jinya a Gunners.
A wata fira da manema labarai, Mesut Ozil yace; “Ina matukar farin cikin sosai, Allah ya bani damar sa rigar jasi ta Fenerbahce. Zan saka rigar da alfahari kuma in bai wa kungiyar komai da take bukata a wajena.
Tsohon dan wasan gaba na Jamus Ozil ya ce zai tafi zuwa Istanbul tare da danginsa a ranar Lahadi da yamma, wanda hakan zai kawo karshen dangantakar shekaru bakwai da rabi da yayi a Arsenal wacce ta yi tsami a karkashin kocin kungiyar na yanzu Mikel Arteta.
Dan wasan mai shekaru 32 bai buga wa kungiyar Premier wasa ba tun watan Maris na 2020 kuma kwantiraginsa da aka ruwaito kan albashin mako-mako £ 350,000 ($ 475,000) an shirya zai kare a karshen wannan kakar ta bana.
A karshe Ozil yayi ikirarin cewa yana cikin koshin lafiya duk da cewa ya jima bai taka leda ba.