fbpx
Friday, July 1
Shadow

Miji ya gantsarawa matarsa cizo saboda ta ki yadda ya kwanta da ita

Wata  mata a Diobu dake jihar Rivers me suna Rose ta gamu da cizo a yatsa bayan da ta hana mijinta yayi kwanciyar aure da ita.

 

Mijin me suna Moses dan kimanin shekaru 42 ya ciji matarsa inda suka fito kan titi sunata sa’insa abinda ya dauki hankulan makwabta wasu cike da mamai wasu kuma nata dariya.

Moses ya amince cewa ya ciji matarsa inda yace saboda zaman gidane da gwamnati tasa a yi dalilin cutar Coronavirus/COVID-19 shiyasa baya iya ciyar da matar tasa ita kuma taki yadda ya kwanta da ita.

Karanta wannan  IKON ALLAH: Wata Mata Ta Haifi ‘Yan Hudu, Dukkansu Mata A Babban Asibitin Shinkafi Dake Jihar Zamfara

 

A nata Bangaren Rose tace duk dai gari na kulle ai sauran sa’annin mijinta na can na nemawa iyalansu abinci ta hanyoyi daban-daban,  sai shine yanzu ya zauna a gida kullun kawai sai yace sai ya kwanta da ita Alhalin cikinta babubkomai.

 

Tace suna da ‘ya’ya 3 amma maimakon Moses ya fita ya samo musu abinci yaki, saidai jim’ai,  dan haka ta gaji.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.