fbpx
Friday, December 2
Shadow

Mijin dazai aureta ya fasa saboda kwamen dinta a “Facebook”!

Daga Tonga Abdul Tonga

Wani saurayin da aka samusu rana da wacce zai aura. Ya fasa auren mako guda a daura musu auren saboda sharhin data yi a shafin Facebook.

Budurwar tasa ta shiga wani shafi ne da aka nemi jin ra’ayin mata ko zasu iya cin amanar mazansu akan naira miliyan 1? A yayin ta rubuta koment tace,” Sosai kuwa zan iya cin amanar mijina. Miliyan 1 na naira fa ba karamin kudi bane”. Wannan ra’ayin nata ya jawo mata bakin cikin dana sani bayan wani da yasanta yake abota da wanda zai aureta yayi tagging dinsa a koment din nata. Wanda hakan ya kawo karshen shirinsa na aurenta.

Wannan lamarin daya dace mata su dauki darasi akansa na yadda suke kuskuren wajen rubuta wasu abubuwan da zai iya jawo musu yin da sun sani.

Mene zaku ce ?.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *