Mijin matarnan da ‘ya’yanta 2 masu idon kyanwa, Rasikat Azeez da ta yi ikirarin cewa ya koresu saboda kalar idanunsu a karin farko yayi magana.
Abdulwasiu Omo Dada ya bayyanawa Punch a hirar da ta yi dashi cewa, matarshi karya ta fadawa ‘ya jarida.
Yace ba saboda idanunta suka rabuba. Yace yana iya bakin kokarinsa wajan kula dasu ita da ‘ya’yanta amma maganar gaskiya ba dan idonta ya rabu da ita ba.
Ya zargeta da iyayen ta da saka hotunan ‘ya’yansa a shafukan sada zumunta dan neman kudi yace amma shi bai taba neman tallafi dan ciyar dasu ba.
Matar dai ta samu tallafi har daga matar gwamnan jihar Kwara da wasu ma daga kasashen waje.