Uwar gidan gwamanan jihar kaduna Hadiza Isma’il El’rufai ta yi maratani ga masu sukanta a dandalin kafar sada zumunci dake tuwita Inda ta bayyana cewa ita tana auran gwamnane kawai amma ba’itace gwamna ba.
Sukar ya faru ne tun bayan bayyana murnar, da matar gwamnan tai na samun mabiya Kimanin 80,000 a shafinta na kafar sada zumanta dake tuwita, inda wasu ke sukarta da cewa zaifi kyautuwa tai magana akan al’ummar kudancin jahar kaduna bisa rikice rikican dake addabar yankin.
Rahotanni baya bayannan sun bayyana cewa fiye da mutane 12 ne aka kashe a makon da ya gabata a Kajuru lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani ƙauye.
Sai dai a lokacin datake martani kan lamarin kashe-kashan matar gwamanan ta bayyana cewa “bana batutuwa masu muhimmanci kamar mulki da siyasa a dandalin kafar sada zumunta, inda ta kara nanata cewa ita matar aure ce wacce kuma mijin ta yake gwmana amma “banice gwamanan ba. Inji ta