Saturday, March 28
Shadow

Mikel Arteta ya warke daga coronavirus

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce ya warke sarai daga coronavirus da ya kamu da ita.

 

 

Dan kasar Spaniya, mai shekara 37, ya zama kocin Premier na farko da ya kamu da coronavirus ranar 12 ga watan Maris.

 

 

Kocin ya sanar da baya jin dadin jikinsa, bayan da aka tabbatar ya yi cudanya da mai Olympiokos, Evangelos Marinakis wanda ya kamu da cutar ranar 10 ga watan Maris, inda Arsenal ta buga Europa League da kungiyar ta Girka.

 

 

Arteta ya ce ”Sai da na yi kwana uku zuwa hutu ina jinya sannan na fara jin karfin jikina, daga nan alamun cutar ya bace”

 

 

Ranar Talata ya kamata ‘yan wasan Arsenmal su koma atisaye, bayan da aka killacesu mako biyu, saboda samun Arteta da coronavirus, an kuma dage ranar da za su koma karbar horo.

 

 

Arsenal ta ce ”Bai kamata cikin wannan yanayin da ake na fargaba a bukaci ‘yan kwallo su koma fagen fama ba.

 

 

”Saboda haka kungiyar kwallon kafarmu ta maza da ta mata da ta matasa za su ci gaba da zama a gida har sai an bukaci su koma taka leda.”

 

 

‘Yan wasan Arsenal da dama ne suka killace kansu, bayan labarin Marinaki na dauke da coronavirus a lokacin Arsenal na shirin fuskantar Manchester City a gasar Premier ranar 11 ga watan Maris.

 

 

Tuni dai aka dakatar da dukkan wasannin gasar kwallon kafar Ingila zuwa cikin watan Afirilu idan an samu saukin coronavirus.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *