Wednesday, June 3
Shadow

Mikel Arteta yace ilimintar da yan wasan premier lig gami da cutar Covid-19 na da matukar muhimmanci

An dakatar da wasannin kwallon kafa a kasar ingila saboda rikicin cutar coronavirus, amma an samu labari ranar talata cewa ministoci suna iya bakin kokarin su domin suga cewa an cigaba da buga wasannin yayin da gwamnatin kasar ke shirin sassauta dokar zaman gida.

Shugaba Arsenal Arteta wanda bai dade da warkewa daga cutar ba yace babbar matsalar da premier lig zasu fuskanta wajen dawowa shine ilimintar da yan wasan su da kuma sauran ma’aikatan su gami sababbin sharuddan cutar Covid-19.
Daya daga cikin dokokin da premier lig tasawa yan wasan ta shine zasu rufe fuskokinsu idan aka cigaba da yin atisayi, yayin da suma kungiyoyin nasu zasu siyo abun rufe fuskan dayawa su ajiye saboda tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *