fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Mikel Arteta zai siyar da wasu yan wasan shi 2 dan yiwa Aubameyang sabuwar kwangila

Manajan Arsenal Mikel Arteta ya san cewa in har suka ce zasu yiwa Aubameyang sabuwar kwangila to zata yi tsada saboda haka ne suka yanke shawarar siyar da yan wasan su har guda biyar domin su cigaba da wasa tare da tauraron nasu.

Kwangilar Aubameyang zata kare ne nan da shekara daya kuma Arsenal suna tattaunawa gami da sabuwar kwangilar da zasu yi mai no kuma su siyar da shi a wannan kakar wasan inba haka ba zai bar kungiyar a kyauta da zarar kwangilar shi ta kare.
Arsenal zasu iya karama tauraron nasu kwangilar shi in har suka siyar da Shkodran Mustafi da Henrikh mkhitariyan a wannan kakar wasan a cewar tsohon dan wasan su da kuma dan wasan Scotland da mai yin sharhin wasanni kwallon kafa Charlie Nicholas.
Arsebal sun siyo Aubameyang ne daga Borussia Dortmund a shekara ta 2018 a farashin da basu taba siyan wani dan wasa ba euros miliyan 56, kuma tun da suka siyo yana kokari sosai yanzu haka a wannan kakar wasan yayin nasarar jefa kwallaye har guda 20 a wasanni guda 32 daya buga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

Leave a Reply

Your email address will not be published.