fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Miliyan 100 da ‘yan siyasa ke fitarwa su sai fom din takara ka iya tunzura matasa su aikata laifuka>>Sheikh Gumi

Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, Miliyan 100 da ‘yan siyasa ke fitarwa suna sayen fom din takarar APC ka iya tunzura matasa.

 

Yace hakan sam bai dace ba yayin da ake tsare da wasu ‘yan Najeriya ana neman wai sai an biya kudin fansa kamin a sakesu.

 

Yace cikin ‘yan siyasar babu wanda ya tara kudi dan ya biya kudin fansa a saki wadanda aka yi garkuwa dasu.

 

Hakanan yace irin wannan kudi da ake ta wasa da su ka iya tunzura matasa su shiga aikata miyagun laifuka dan suma su samu irin wadannan kudade.

 

Ya bayyana hakane a hedikwatar jam’iyyar matan Arewa yayin wani taro da aka yi tsakanin Kiristoci da musulmai dan yiwa wadanda aka yi garkuwa dasu din Addu’a.

 

Sheikh Gumi ya kuma kara da cewa, dangin wadanda aka sace din ba su kadai ne ke bakin cikin hakan ba, duka Najeriya na bain cikin wannan lamari.

Karanta wannan  Mutum 32 'yan Iswap suka kashe a Kala-balge a Borno

 

Ya tabbatar musu da cewa, nan ba da dadewa ba za’a sako danginsu da aka kama.

 

“I have not heard of any leader raising money to free any kidnapped victim(s) or the 62 abducted passengers.

“I have been in the forefront in trying to see that all these things are resolved. Initially the issue was socio economic, but now it is taking a religious dimension due to the negligence of the government. Can’t they raise money too to free these 62 Nigerians including the 85 year-old woman? Please whatever the bandits or terrorists want from government, government should endeavour to give them in the interest of captives and Nigerians because their continued captivity is not in our interest,” he said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.