fbpx
Friday, August 12
Shadow

Milyoyin kudin da PSG zata ba kocinta Pochettino don ya sauya sheka sun bayyana

Makudan kudaden da kungiyar Paris Saint Germain zata ba kocinta Mauricio Pochettino bayan ya amince ya bar kngiyar sun bayyana.

PSG bata son kocin ya cigaba da horas da ‘yan wasanta wanda hakan yasa ta bukaci ya suya sheka, amma yace dole sai ta biya shi saboda yana sauran kwantirakin shekara guda.

Wanda hakan yasa ta amince ta biya shi yuro miliyan goma don ya hakura da kwantorakin nashi daya rage.

Kocin kungiyar Nice, Christophe Galtier ne zai cigaba da horas da PSG, bayan Pochettino ya kasa taimakawa kungiyar ta lashe kofin Lig 1 a kakar data gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.