Karamar Ministar, Babban Birnin Tarayya Abuja Ramatu Tijjani Aliyu ta ba da takardar shaidar girmamawa ga membobin Hukumar NYSC 25 saboda gagarumar gudummawar da suke bayarwa wajen yakar cutar Corona (COVID 19).
An sanar da hakan ne yayin gabatar da takardar shaida ga mambobin kungiyar jiya a Abuja.
A cewar wakiliyar ministar Kula da ci gaban jama’a ta FCT, Dilichukwu Onyedima ta ce, mambobin kungiyar sun yi rawar gani a yayin wannan annoba ta COVID 19 saboda sun sami damar samar da abin rufe fuska, dana wanke hannu sannan kuma sun sami dabaru da horo da yawa sa’annan suka wayar da kan al’umma ta hanyar horon da suka samu.
Haka zalika ta kara da cewa “Munyi hakan ne don mununa godiyar mu bisa namijin kokarin da mambobin suka aiwatar a wannan lokaci wanda abunda sukai zai taimaka musu wajan zama ‘yan kasa Nagari. A cewarta