Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a safiyar ranar Juma’a, ya rasa mahaifiyarsa, Hajia Fatima Adamu Gamawa, tana da shekara 107.
Mirigayyar ta rasu ne ta bar yara shida – maza uku da mata uku- Malam Lawal Adamu, Hon. Ibrahim Adamu, dan siyasa a Bauchi, Malam Adamu Adamu, Hajia Hafsat Mohammed, Hajia Hauwa’u Taudo da Hajia Iya Abubakar- da kuma jikoki da yawa.