Ministar kula da ayyukan jinkai, Hajiya Sadiya Umar Farouk a ranar Litinin, ta ki amincewa a karo na hudu, bisa gayyatar da kwamitin Majalisar Wakilai yai mata domin yin bayani game da yadda ofishinta ya gudanar da rarraba kudaden da aka kebe don talafawa marasa galihu a sakamakon barkewar cutar coronavirus a Najeriya.
An nemi ministar ta bayyana a gaban kwamitin majalisar don ta yi bayani dalla-dalla yadda aka rarraba kudaden da aka bai wa ma’aikatar da cibiyoyi da hukumomin da ke karkashin kulawarta.
Sai dai rashin amincewar amsa gayyatar da majalisar taiwa ministar, ya saba wa sashi na 4, 81, da 88 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999. Wanda ya baiwa majalisar ikon yin bincike a kan kowa wanda ya hada da Shugaban Tarayyar kasa da kuma Ministocinsa da shugabannin hukumomin gwamnati.
Shugaban kwamitin, Wole Oke mai wakiltar jam’iyyar PDP a jihar Osun da sauran membobin Kwamitin, sun nuna rashin jin daɗin su ga yadda Ministan ke raina majalisar.