fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ministan Lafiya na Ghana ya kamu da korona

Rahotanni daga Ghana sun ce gwaji ya tabbatar da ministan lafiya na ƙasar ya kamu da cutar korona.

Shafin Ghanaweb ya ce ministan Kwaku Agyeman Manu tun makon da ya gabata aka kwantar da shi a asibitin Jami’ar Ghana a Accra amma yana samun sauki.

Jaridar ta ce shi ne babban jami’in gwamnati na farko da ya kamu da korona a ƙasar Ghana wanda kuma ke jagorantar yaƙi da cutar a ƙasar.

Wannan na zuwa a yayin da wasu rahotanni suka ce wasu daga cikin ƴan majalisar Ghana gwaji ya tabbatar da suna ɗauke da cutar korona inda kuma suka ƙi killace kansu a gidajensu.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Zuwa yanzu sama da mutum 11,000 aka tabbatar da sun kamu da korona a Ghana yayin da cutar ta kashe mutum 48.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.