fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ministan sadarwa, farfesa Isa Pantami yayi watsi da shirin da gwamnatin Buhari keyi na kara haraji akan kiran waya, data da kuma tura sakonni

Ministan sadarwa na kasa, Farfesa Isa Pantami yayi watsi da shirin da gwamnatin Buhari keyi na kara haraji akan kiran waya da sayen data da kuma tura sakonni.

Sheik Isa Pantami ya bayyana hakan ne a taron da suka gudanar a jihar Legas kan wannan batun na kara kudin harajin da masu hannu da tsaki na kamfanin layukan waya.

Inda yace shi babu wansa ya nemi shawararshi akan wannan harajin da ake shirin karawa akan layukan waya.

Kuma shi baya goyon bayan hakan domin bai kamata gwamnati ta karawa talakawa wani nauyi akan su saboda dama can akwai haraji akan layukan wayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.