Ministan sadarwa, kuma shehin Malamin Addinin Islama ya karyata zarcin aikata ba daidai ba da kudi da aka ma ma’aikatarsa ta Sadarwa da Tattalin arzikin zamani.
Jaridar Sahara Reporters ce ta wallafa cewa ministan yaje yana duba kwamfutocine da za’a yi amfani dasu wajan ganawar jami’an gwamnati amma kuma kwamfutocin na amfanine da manhajar Window 7.
Labarin ya kara da cewa wannan fa na faruwane duk da makudan kudin da aka warewa ma’aikatar ta Sadarwa a shekarar 2019 da suka kai Naira Biliyan 17.
Saidai a martanin malam ya bayyana cewa wannan ba gaskiya bane, babu jami’in gwamnatin dake amfani da manhajar Window 7 wajan ganawa.
Ministan ya kara da cewa, gaba dayan kudin da aka baiwa ma’aikatarsa ta yi amfani dasu wajan aiki a shekarar 2019 basu kai Naira Biliyan 1.5 ba.
Ya kara da cewa kuma shi wannan majigi da ake ganinsa a gabanshi bama a hadashi da yanar gizo ba tukuna
THIS IS NOT TRUE:1)No government official uses Windows 7 for videoconferencing; 2) Entire capital released of & @FMoCDENigeria in 2019 is less than N1.5billion including constituency projects; & 3)The screen is standalone, & not even connected to d internet,& not for the Mins https://t.co/xhCSpY72WZ
— Isa Ali Pantami, PhD (@DrIsaPantami) May 20, 2020
A baya dai ministan yayi gargadin amfani da Manhajar Window 7 saboda yace kamfanin Microsoft sun daina sabuntata dan haka akwai hadarin ajiye bayanai a ciki.