fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Ministan Tsaro ya bukaci matasa da kar su yarda a yi amfani da su wajen haddasa fitina a kasa

Ministan Tsaro ya bukaci matasa da kar su yarda a yi amfani da su wajen haddasa fitina a kasa

Ministan Tsaro mai ritaya Manjo.-janar Bashir Magashi ya bukaci matasa da kar su yarda a yi amfani da su wajen lalata tsaro da haddasa fitina a kasar.

Magashi ya yi wannan kiran ne a taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a ranar Asabar don inganta zaman lafiya a jihar Kano.

Ya ce kiran ya zama wajibi ne domin samar da zaman lafiya a jihar da kuma kasa baki daya.

A cewar sa, “A makonni biyu da suka gabata kasar ta tsinci kanta cikin zanga-zangar da wasu matasa suka gudanar don nuna adawa da rundunar ‘yan sandan SARS, sai dai daga bisani lamarin ya canza salo inda wasu bata gari su ka shiga al’amarin daga karshe hakan ya zama fitina wanda ya janyo asarar rayuka da dokiyoyin jama’a.

Magashi ya kuma yi kira ga matasa da su guji mummunan ra’ayi da son zuciya wadanda za su kawo barazana ga tsaron kasa.

Ya ce kasar na fuskantar kalubalen ‘yan fashi, satar shanu, satar mutane da rikicin Boko Haram da sauransu.

Ministan ya jaddada bukatar sadaukar da kai don tallafawa kokarin gwamnati na kiyayewa da kare martabar kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *