Saturday, July 13
Shadow

Ministan yaƙin Isra’ila ya sauka daga muƙaminsa

Ministan yaƙi na Isra’ila, Benny Gantz ya fice daga cikin gwamnatin Netanyahu.

Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai, Mista Gantz ya ce firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya ƙi bari a samu abin da ya kira ‘tabbatacciyar nasara’ kan Hamas.

Ministan ya ƙara da cewa dole ne Mista Netanyahu ya sanya ranar da za a gudanar da zaɓukan ƙasar.

Tun a ranar Asabar mista Gantz ya yi niyyar gabatar da jawabin nasa, to amma sai ya jinkirta saboda kuɓutar da wasu Isra’ilawa da sojojin ƙasar suka yi a Gaza.

Ficewar jam’iyyarsa daga gwamnatin, ba zai kawo ƙarshen gwamnatin ba, to amma zai ƙara matsin lamba kan mista Netanyahu kan sukar da yake sha a ciki da wajen Isra’ila.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu:Kasar Faransa ta hana kasar Yahudawan Israela zuwa bikin nuna makamai saboda kisan Falas-dinawa

Dama dai tun cikin watan Mayun da ya gabata, Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yaƙin ƙasar idan Netanyahu ya ƙi bayyana shirinsa na kula da zirin Gaza bayan yaƙin da suke yi da Hamas ya zo ƙarshe.

A ranar 19 ga watan Mayu, Mista Gantz ya ɗebar wa gwamnatin Netanyahu wa‘adin ranar 8 ga watan Yuni domin tsara manufofi shida ciki har da kawo ƙarshen mulkin Hamas a Gaza da kuma kafa gwamnatin farar hula da duniya za ta aminta da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *