fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ministar lafiyar Burtaniya ta kamu da coronavirus-Covid-19

Ministar lafiyar Burtaniya Nadine Dorries ta kamu da cutar Coronavirus.

Ministar ta sanar da cewa a yanzu ta killace kanta, yayin da hukumomi ke ta kokarin gano inda takwaso cutar.

Ko a ranar Alhamis ta halarci wani taron cin abinci da Firanminista Boris Johnson ya shirya a fadar gwamnati da ke titin Downing.

Wakilin BBC ya ce hukumomi na kokarin gano wadanda ministar ta yi mu’amala da su.

Kusan mutun 400 ne cutar coronavirus ta kama a Birtaniya inda shida suka mutu.

Misis Dorries ta ce ta damu matuka kan makomar lafiyar mahaifiyarta mai shekary tamanin da hudu wacce a hanzu haka suke zaune a gida daya.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.