fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Miyagu na nan suna shirin tada bamabamai, ku kiyaye>>DSS ta gayawa ‘yan Najeriya

Hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta gargadi ‘yan Najeriya da cewa, su kiyaye dan kuwa bata gari na nan suna son saka bamabamai a gurare.

 

DSS tace inda ake shirin kai bamabaman akwai guraren Ibada da kuma guraren shakatawa.

 

Ta kuma ce an shirya kai hare-haren ne yayin da ake shirin fara bukukuwan sallah karama wadda za’a yi bayan Azumin watan Ramadana.

 

Kakakin hukumar, Peter Afunanya ne ya bayyana haka inda yace masu kula da irin wadannan gurare su saka ido kuma itama hukumar tasu zata hada hannu da sauran hukumomin tsaro dan magance matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.