fbpx
Friday, July 1
Shadow

“Miyagun mutane ne ke kokarin saka Najeriya cikin rikicin addini”>>Shugaba Buhari akaan harin da ake kaiwa cocina

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa miyagun mutane ne ke kokarin saka Najeriya cikin rikicin addini.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan hare haren da ‘yan bindiga ke kaiwa fastoci da kuma cocina a fadi kasar nan.

Kamar yadda suka je cocin Owo dake jihar Ondo suka kashe mutane da dama kuma suka kara kai wani hari jihar Kaduna da dai sauran su.

Hadimin Buhari, Garba Shehu ne ya wallafa wannan labarin a Twitter, inda yace zaman lafiyar kasar nan nada hadi da hadin kan da addinai keda shi, kuma baza su laminci hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.