Tauraron dan wasan gaba na Liverpool ta kasar Ingila, Mohammed Salah ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar daya ci kwallo a wasannin farko na gasar sau shida a jere.
Mohammed Salah yayi nasarar cin kwallon ne a wasan da suka buga na farko da kungiyar Fulham.
Inda suka tashi daci 2-2, kuma Darwin Nunez ne ya ciwa Liverpool dayar kwallon yayin da Mitrovic shi kuma ya ciwa Fulham kwallayen guda biyu.