Tauraron dan wasan Liverpool Mohammed Salah ya kai hare hare masu kyau har guda shiga a wasan su da Madrid daren jiya, amma Courtoi yayi nasarar cire su duka.
Inda ya zamo dan wasa na farko daya kai hari sau shida a wasan karshe na gasar zakarun nahiyar turai tun kakar 2003-2004.
Yayin da shima mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtoi ya zamo gola na farko daya nasarar cire kwallaye tara a wasan karshe na gasar tun kakar 2003-2004.