fbpx
Monday, August 15
Shadow

Monckeypox ba Covid-19 bace ba za’a saka dokar kulle akanta ba, cewar darekta janar na hukumar NCDC

Darekta janar na hukunar dake lura da cututtuka a Najeriya watau NCDC, Afedayo Adetifa ya bayyana cewa ba za’a saka dokar kulle ba saboda cutar Monkeypox.

Darektan ya bayyana hakan ne ranar talata a wani taro da suka gudanar inda yace ita cutar ba kamar Covid-19 bace domin sunada ilimi akanta.

Amma ita kuwa Covid-19 basu da ilimi akanta ne sai yasa aka saka dokar kullle din ayi bincike akan cutar.

Ya bayyana hakan ne bayanda wasu ‘yan Najeriya ke bayyana cewa da yiyuwaa a sake saka dokar kulle kan cutar domin tayi kamari a kwanakin nan, amma ya musanta hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.