fbpx
Friday, July 1
Shadow

Motar Cristiano Ronaldo ta Bugatti Veyron mai farashin yuro miliyan 1.7 tayi hatsari a Majorca

Daya daga cikin motoci biyu na alfarma da tauraron dan wasan tamola na kungiyar Manchester United, Ronaldo ya kai sabon gidansa na Majorca tayi hatsari.

Motar ta kasance kirirar kamfanin Bugatti Veyron mai farashin yuro miliyan 1.7, kuma direban baiji rauni gaban motar ne ya samu matsala.

Wani ma’aikacinsa ne ke tuka motar yayin da wannan hatsarin ya faru  misalin karfe 11 na safiyar yau litinin.

Kuma hukumar ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike akan lamarin, amma har yanzu basu bayar da wani karin bayani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.