fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Motocin a Kori kura da Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano inda suka nunka kudin daukar Fasinja

Motocin a Kuri kura da Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano

 

Tun da safiyar yau ne dai aka wayi gari da yajin aikin masu Adai-daita sahu a jihar Kano inda ya tilastawa mutane da yawa hawa akori kura da domin fita wuraren kasuwanci da ayyukansu na yau da kullum ko kuma mutum ya tafi a kafa.

 

A zagayen da wakilin Hutudole ya gudanar ta gano yadda mutane ke rigegeniya wajen hawa a kori kura a wurare da dama ko kuma su rasa abin hawa.

 

Manyan hanyoyin da aka gano masu hawa akori kurar na rububi sun hadar da sabon titin Mandawari zuwa Kwari da Kurna zuwa Ibrahim Taiwo da kuma titin Panshekara zuwa Kofar Fanfo.

 

Haka zalika an gano wasu akan titin Kofar Ruwa zuwa filin jirgin sama zuwa kasuwar Sabon Gari da wasu tituna daban-daban na cikin birnin Kano.

 

Su kansu masu kurkurar jamaa sun koka akan yadda su yan kurkurar suka ninka kudin hawan, inda suka ce ko a adaidaita inda suke biyan 100 amma yanzu a Kurkura 300 suke karba.

 

Masu Adaidaita Sahu a kano dai sun fara yajin aiki ne tun bayan da gwamntin Kano ta ce sai sun bayar da harajin shekararar da ta gabata da kuma na kullum naira Dari dari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *