Kamfanin Femadec Group da haɗin gwiwar Gwamnatin Taraiya za su fara kawo motocin bas masu amfani da iskar gas a ranar 5 ga watan Mayu domin fara haya a birnin Abuja.
Shugaban kamfanin, Fola Akinnola ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawa da NAN a jiya Laraba a Legas.
Akinnola ya ce matakin wani ɓangare ne na aiwatar da manufar Gwamnatin Taraiya ta samar da motocin sufuri masu amfani da iskar gas wa ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar s watan Disambar 2020.
A cewar sa, Femadec Express, wani reshe na kamfanin Femadec Group shi ne zai tafiyar da hayar motocin, inda ya ƙara da cewa za a fara ne da motocin bas 20.
Ya kuma baiyana cewa kamfanin Hyundai ne ya ƙera motocin a Koriya ta Kudu.
Ya ce tuni shirye-shirye su ka yi nisa wajen ƙaddamar da sabon tsarin sufurin, inda ya baiyana cewa a na nan a na horas da direbobin da za su tuƙa motocin, sannan a na saka tsarin biyan kuɗin mota na zamani a cikin motocin.
“Mun haɗa kai ne da kamfanin sufurin motoci na Abuja domin samun sauƙin aiwatar da shirin,” in ji shi.