fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Mourinho: Messi ya amince da komawa Chelsea a shekara ta 2014

Maganar da Messi yayi na barin kungiyar Barcelona a kakar data gabata ta girgiza duniyar wasan kwallon kafa sosai, amma sai dai ba kowa ne yasan cewa wannan bashi ne karo na farko da dan wasan Argentinan ya bukaci barin kungiyar ba.

Dan jarida na kasar Italiya Gianluca Di Marzo ya bayyana cewa kiris ya rage Messi ya koma kungiyar Chelsea a shekara ta 2014 wadda Barcelona ta kasa lashe babban kofi a kakar karkashin jagorancin Gerardo Martino, wanda ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Spanish Super Cup amma aka cire ta a gasar Champions League kuma ta fadi wasannin karshe na La Liga da Copa del Rey a hannun Atletico da kuma Real Madrid.
Dan jaridar ya kara da cewa Messi ya gana da Jose Mourinho a lokacin kuma har dan wasan mai shekaru 33 ya amince da komawa Chelsea wadda take shirin biyan farashin sa na yuro miliyan 250 tare da kuma albashin yuro miliyan 50 a kowace shekara. Amma sai dai mahaifin Messi Jeorge tare da kuma shawarar tsohon dan wasan Barceona Deco ne suka hana shi komawa Premier League a shekarar.
A karshe Di Marzo yace shugaban Real Madrid Florentino Perez shima yayi yunkurin siyan Messi a shekarar 2013 amma dan wasan Argentinan yaki amince da fara tattaunawa da babban kungiyar hamayyar Barcelonan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *