Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna, Farfesa Andrew Jonathan Nok ya mutu yau bayan gajeruwar rashin lafiya, a lokacin rayuwarshi ya kafa tarihin da Duniya ba zata taba mantawa dashiba, shine mutum na farko a Duniya da ya fara gano maganin ciwon bacci wanda a turance ake kira da (Sleeping Sickness).