fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

“Mu ba yan ta’adda bane, MURIC ta musanta alaqa da Kungiyar ISWAP

Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC), a ranar Talata, ta ce ba ta da wata alaƙa da wani gungun ‘yan ta’adda a ciki da wajen Najeriya.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar Legas.

Akintola ya bada tabbacin cewa, kungiyar Ku kadan bata da wata alaka, ta kusa ko ta nesa tsakanin ta da ko wacce kungiyar ta’addanci.

Ya kuma  jawo hankali Mutane tare da karyata jita jitar da a ke yadawa cewa kungiyar ta karbi Dala 200,000 daga kungiyar ‘yan ta’addan (ISWAP).

Karanta wannan  An kama 'yansandan boge 5 a jihar Nasarawa

Akintola ya bayyana cewa “Kungiyar Kare hakkin Musulmai ta Najeriya kungiya ce ta hada kai, kuma kungiyar na Allah wadai da duk wani aiki na ta’addanci A Najeriya dama Duniya baki daya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.