fbpx
Monday, December 5
Shadow

MU GUDU TARE MU TSIRA TARE>>Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Kayi Ibada akan sharudai guda biyu:
1. Yinta da Ikhlasi.
2. Ynita akan Sunnah.
*Ka nemi yarda guda biyu
1. Yardar Allah.
2. Yardar Iyaye.
*Ka roqi abubuwa guda biyu
1. Samun Rahamar Allah.
2. Tsira daga Azabar Allah.
*Ka kare abubuwa guda biyu.
1. Addinin ka.
2. Mutuncin ka.
*Ka yaqi abubuwa guda biyu:
1. Jahilci.
2. Talauci.

*Kaci moriyar abubuwa guda biyu:
1. Lokaci.
2. Lafiya.
*Ka yawaita tunanin abubuwa guda biyu:
1. Kwanciyar Kabari.
2. Tashin Alkiyama.
*Ka tabbatu akan abubuwa guda biyu:
1. Fadar gaskiya.
2. Rukon Amana.
*Ka rage abubuwa guda biyu:
1. Yawan cin abinci.
2. Yawan bacci.
*Ka yarda da abubuwa guda biyu:
1. Qaddara mai kyau.
2. Qaddara mara kyau.
*Ka fifita soyayya guda biyu:
1. Son Allah.
2. Son Manzon Allah.
*Ka siffantu da dabi’u guda biyu:
1. Ganin girman na sama.
2. Tausayawa na kasa.
*Ka nemi tsarin abubuwa guda biyu:
1. Shedanun cikin Aljanu.
2. Shedanun cikin Muatane.
*Ka sadaukar da rayuwar akan abubuwa guda biyu:
1.Neman ilimi.
2. Yin aiki da ilimi.
*Ka shige gaba a wajan abubuwa guda biyu:*
1. Aikin Alkhairi.
2. Kira ga Alkhairi.
*Ina fatan zakuyi abu biyu:*
1. Aiki da abinda saqon ya qunsa.
2. Turawa ‘yan uwa domin su amfana

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Ɗalibin nan Aminu Adamu ya koma makarantarsu ta jami'ar tarayya da ke Dutse domin ci gaba da karatu bisa rakiyar ƴan ƙungiyar dalibai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *