fbpx
Friday, July 1
Shadow

Mu ne muka kaiwa Gwamna Zulum hari>>IS

Wasu da ake zargi masu iƙirarin jihadi ne sun sake kai wa tawagar gwamnan Borno Babagana Zulum hari dai-dai lokacin da suke komawa Maiduguri, babban birnin jihar.

Gwamnan ya tsira da ga hari na ranar Lahadi sannan ba a samu asarar rai ba.

Babu tabbaci kan ko gwamnan yana cikin tawagar.

Harin dai ya faru ne kusan sa’a 48 bayan da masu ta da ƙayar bayan suka afkawa tawagar gwamnan a yankin Baga inda kimanin mutum 30 suka mutu a harin – har da sojoji da ƴan sanda.

Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai harin.

Gwamna Zulum ya kai ziyara yankin Baga a ƙoƙarin da ake na maido da dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita matsugunansu.

Karanta wannan  'Yansanda sun kashe 'yan Bindiga 2 a Anambra

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan tawagar gwamnan.

Ya bayyana harin a matsayin maƙarƙashiya ga shirin da ake yi na ganin mutanen da rikici ya ɗaiɗaita sun koma gidajensu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.