fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Mudai ba zamu kori Almajirai ba, inganta karatunsu zamu yi>>Gwamnatin Sokoto

Sabanin matsayar da gwamnonin arewacin Najeriya suka cimma ta mayar da almajirai jihohinsu na haihuwa, gwamnatin jihar Sakkwato tace ba za ta kori kowane almajiri ba.

 

 

A cewar gwamnatin za ta dai inganta tsarin na karatun alkur’ani ta yadda ba sai yara sun tafi yawon barace-barace ba.

 

Dr Umar Altine Mahe, shi ne sakataren kula da hukumar ilimin larabci da adinin musulunci a jihar kuma shi ya tabbatar da lamarin a hirar shi da Sashen Hausa.

 

 

“Mu bamu da niyyar korar almajiran nan, ilimi ai ilimi ne, saboda haka dole mu gyara tsarin karatun.”

 

 

A baya ma ana ta daukar matakai na kyautata wa tsarin amma hakan bai hana yara fita barace-barace ba.

 

 

A wannan karon dai gwamnati ta ce, wannan sabon tsarin an dauko shi ne daga kasar Indonesia kuma suna sa ran zai taimaka.

Karanta wannan  Shugaban kasa, Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima zasu kashw Naira Biliyan 15 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

 

 

Farfesa Tukur Muhammad Baba, masani ne kuma ya sheda wa Muryar Amurka cewa “yunkurin nan da gwamnatin sokoto ta yi, abin yabawa ne kuma abin da ya kamata a yi ne tun tuni.”

 

 

Dangane da zancen almajiran dai, 11 daga cikin wasu almajirai 33 da aka dawo da su daga Zaria, suna dauke da cutar Coronavirus a cewar kwamishinan lafiya na sokoto Rr Muhammad Ali Nnname.

 

 

Lamarin da ya mayar da hannun agogo baya, a lokacin da jihar ta fara murnar cewa babu mai dauke da cutar a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *