Tsohon gwamnan Anambra, ChuKwuemeka Ezeife yayi gargadin cewa muddin dan Arewa ya zama shugaban kasa a 2023 to Najeriya ba zata dore ba.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da Sahara Reporters inda yace yana baiwa jam’iyyun APC dana PDP shawarar su tsayar da dan kudu a zaben 2023.
Yace yana jin rade-radin cewa Arewa ma na son tsayawa takara. Yace muddin Arewa na so Najeriya ta ci gaba da dorewa to sai fa a baiwa dan kudu mulkin kasarnan a 2023.
Yace amma duk da rikicin dake daruwa a APC da wuya hakan ya shafi zaben 2023 dan rikin jam’iyya baya dorewa.