fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Muhimman abubuwa huɗu da za su faru a wajen taron fitar da gwani na APC

A yayin da APC ta ɗau harama a zaɓen fitar da gwaninta na mutumin da zai tsaya takara a inuwar jam’iyyarta, ga wasu muhimman abubuwa da ake saran su faru a wajen taron.

Tantace Daliget

Da misalin karfe 10 na safe har zuwa 1 na rana ake soma tantace masu jefa kuri’a a wannan zaɓe da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya. Wadannan daliget su za su yanke hukunci da zaɓo mutumin da zai tsaya da tikitin APC a zaɓen 2023.

Jawaban ‘yan takara

Da misalin karfe 4:45 na yamma zuwa 5:45 ake sa ran ‘yan takarar da za su fafata a zaɓen su gabatar da jawabai a wajen taron. Jawaban nasu ana saran ya kasancewa kunshe da batutuwan da za su iya jan hankali masu zaɓe da kuma al’ummar kasa.

Kaɗa ƙuri’a

Za a shafe kusan sa’a uku ana kaɗa kuri’a tsakanin daliget sama da dubu biyu. Da misalin 6:00 na yamma zuwa 9:00 na dare.

Karanta wannan  'yan sanda sun kashe dan bindiga a jihar Kaduna sun kwace babur dinsa da AK47

Sannan za a shafe sa’a 1 wajen kidaya kuri’a. Da misalin 9 zuwa 10 na dare.

Jawabin wanda ya yi nasara

Wannan kusan shi ne abu na ƙarshe da ake saran duk mutumin da ya yi nasara zai gabatar da zaran an kammala kidaya kuri’a da sanar da sunnan wanda ya yi nasara.

Ana dai sa ran duk wanda ya yi nasara ya gabatar da wannan jawabi da misalin karfe 10 na dare.

Zuwa 11 na dare dai ake saran karkare taro. Sannan ‘yan kasa su kuma jiran babban zaɓe a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.