fbpx
Monday, August 15
Shadow

Mulki akwai wahala, na kosa 2023 ta yi in mikawa wanda yaci zabe mulki>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, mulki akwai wahala. Yace ya kosa 2023 ta yi ya mikawa wanda yaci zabe mulki.

 

Shugaban ya bayyana hakane yayin ziyarar gaisuwar Sallah da wasu gwamnoni da ‘yan siyasa suka kai masa a gidansa dake Daura jihar Katsina.

 

Ya kuma kara da cewa,  sauran ‘yan watannin da suka rage, zai yi iya yinsa dan ganin ya kyautatawa ‘yan Najaria.

 

Shugaba Buhari yace nan da shekara me zuwa kamar yanzu idan Allah ya kaimu, ya kammala wa’adin mulkinsa na 2.

Karanta wannan  Luyan Nnamdi Kanu ya zargi gwamnatin Buhari da baiwa 'yan bindiga kulawa ta musamman amma tana tauye hakkin talakawa

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.